Ƙungiyar ma’aikatan hukumar kula da yanayi ta Najeriya (NIMET) sun sanar da janye yajin aikin da suka fara kwana biyu da suka gabata bayan wata ganawa da suka yi da ministan sufurin ƙasar.
Yajin aikin da ma’aikatan suka kira, ya haifar da cikas a filayen jiragen sama na cikin gida inda fasinjoji da dama suka kasa yin balaguro.
Ma’aikatan sun yi yajin aikin ne saboda rashin ingantacen yanayin aiki, rashin gudanar da ayyukansu ya kawo cikas a zirga-zirgar jiragen sama a fadin ƙasar ranar Alhamis
Ma’aikatan sun nuna damuwa kan rashin aiwatar da sabon tsarin albashi mafi ƙaƙanta, da batun wasu alawus-alawus, da kuma yin watsi da muhimman shirye-shiryen horas da ma’aikatan da dai sauransu.
Amma bayan wata ganawa da ministan sufurin jiragen saman ƙasar Festus Keyamo a Abuja, ƙungiyar ma’aikatan ta yanke shawarar janye yajin aikin.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1485 days 18 hours 42 minutes 6 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1467 days 20 hours 23 minutes 31 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com