Boko Haram ta kashe mutum 22 a arewacin Najeriya a ƙarshen mako

Ƙungiyar Boko Haram mai iƙirarin jihadi ta kashe aƙalla mutum 22 a ƙarshen mako sakamakon hare-haren da mayaƙanta suka kai a arewa maso gabashin Najeriya.

A jihar Borno, mayaƙan sun yi wa wasu fararen hula kwanton ɓauna tare da kashe 10 da kuma wasu jami’an tsaro biyu a ranar Asabar, kamar yadda Sarkin Gwoza Mohammed Shehu Timta ya faɗa wa kamfanin labarai na Reuters.

A garin Kopre na jihar Adamawa ma, mayaƙan Boko Haram sun kashe mutum 10 tare da raunata wasu da yawa, a cewar mazauna yankin.

Harin ya auka kan mafarauta ne da kuma mayaƙan sa-kai na CJTF, inda daga baya rundunar ‘yansanda a jihar ta tura ƙarin dakaru, in ji mai magana da yawunta Suleiman Yahaya a yau Litinin.

Najeriya ta daɗe tana fama da mayaƙa masu iƙirarin jihadi, inda Boko Haram da Iswap suka fi kai hare-hare a jihohin Borno da Yobe da Adamawa.

A farkon makon nan ne Gwamnan Borno Babagana Zulum ya koka cewa Boko Haram ta zafafa hare-hare, abin da ke jawo koma-baya a yaƙi da ‘yanbindigar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com