Sojojin dake ƙarƙashin dakarun Operation Hadin Kai hadin gwiwa da Hybrid Forces sun Sami nasarar ne yayin wani kwantan ɓauna da suka yiwa mayaƙan kungiyar ta Boko Haram a kauyen Koibe.
Dakarun sun hallaka mayaƙan guda biyu a karamar hukumar Dikwa dake jihar ta Borno Kamar yadda Jaridar PRNigeria ta ruwaito
Read Also:
Wata majiya daga Rundunar sojin kasar ta tabbatarwa da Zagazola Makama cewa dakarun sojojin sun yiwa ƴan Boko Haram din kwantan ɓauna ƙarƙashin dakarun Operation Desert Sanity IV a yammacin ranar Juma’a bisa rahotannin sirri da ta samu.
Ko dai a safiyar wannan rana gwamnatin jihar Borno ta fitar da wata sanar da ta haramta sayar da man fetur a jihar.