Jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya, NDLEA sun ce sun kama wata mata da ta yi yunkurin fita da hodar iblis zuwa ƙasar Iran.
Wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Femi Babafemi ya fitar, ya ce an kama matar ce a filin jirgin sama a Fatakwal, babban birnin jihar Ribas – inda ta saka hodar iblis ɗin a cikin al’aurarta da cikinta da kuma a wata jaka.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Babafemi ya ce matar mai suna Ihensekhien Miracle Obehi, wadda ta saka hijabi domin ƙoƙarin tsallake binciken jami’an tsaro, an cafke ta ne a Lahadin da ya gabata lokacin da take yunkurin shiga jirgin Qatar Airline zuwa Doha, kafin ta wuce Iran.
Ya ƙara da cewa yayin bincike, an gano matar ta saka ƙunshin hodar iblis har uku cikin al’aurarta, sannan ta saka wani a jakarta sai kuma ta haɗiye ƙwayoyi 67 a cikinta.
Sakamakon haka, an tilasta ta yin aman ƙwayoyin da kuma wanda ta saka a cikinta da al’aurarta.
Obehi ta yi iƙirarin cewa an saka ta ta haɗiye ƙwayoyin hobar iblis 70, sai dai bayan haɗiye 67 ta ƙasa haɗiye sauran – inda ta yanke shawarar saka su a al’aurarta, a cewar Babafemi.










