Rundunar sojin Najeriya ta ce sojojinta na hadin gwiwar Operation Fasan Yamma sun kashe ‘yan ta’adda 10 a jihar Zamfara.
Rundunar ta ce sojojin sun kashe ƴan ta’addan ne a cikin wani mummunan farmaki da suka kai a wuraren da ‘yan ta’addan ke zama a Mai Tashi da Dan Jigba a ƙaramar hukumar Gusau, da kuma Munhaye a ƙaramar hukumar Tsafe a Zamfara, a jiya, 9 ga Yunin 2025.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a shafin sada zumuntarta na X.
A yayin wannan aiki, an ƙwato makamai da dama da alburusai.
Sannan kuma rundunar ta ce an ƙona babura guda 5 da ‘yan ta’addan ke amfani da su a wuraren da aka kai farmakin.