Aƙalla sojoji 34 ne wasu mahara da ake zargin masu ikirarin jihadi sun kashe a Jamhuriyar Nijar, sannan suka jikkata wasu mutum 14.
An kai harin ne a garin Banibangou, wanda ke kan iyakar Nijar da Mali da Burkina Faso, inda ake tunanin akwai mahara masu ikirarin jihadi da suke da alaƙa da ƙungiyar Al Qaeda.
Ma’aikatar tsaron Nijar ta yi Allah-wadai da harin, wanda ta bayyana da “na rashin hankali,”.
Ma’aikatar ta ce “an kai harin ne a ranar Alhamis 19 ga watan Yuni. Wanda hari ne na dabbanci da aka kai a garin Banibangou, wanda wasu mahara waɗanda baƙi ne suka kai a babura sama 200,” kamar yadda ta bayyana a wata sanarwa da ta fitar.
Sanarwar ta ƙara da cewa sojojin ƙasar sun kashe “gomman maharan,” a lokacin da suke musayar wuta, sannan ta tura ƙarin jami’a zuwa yankin.
A yanzu haka dai Nijar da Burkina Faso da Mali suna ƙarƙashin mulkin soji ne waɗanda suka ƙwace mulki bayan hamɓarar da zaɓaɓɓun shugabannin ƙasar, sannan suka kafa ƙawancen tsaro.
Sai dai duk da ƙawancen, har yanzu ƙasashen yankin suna fama da rikice-rikice a ƴan watannin da ake ciki.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1485 days 20 hours 2 minutes 43 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1467 days 21 hours 44 minutes 8 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com