Home General Mutane 5 sun gamu da ajalinsu sakamakon fashewar wani abu a Kano

Mutane 5 sun gamu da ajalinsu sakamakon fashewar wani abu a Kano

Aƙalla mutane biyar aka tabbatar  sun mutu, kana wasu 15 suka jikkata sakamakon fashewar wani abu da ake zargin bam ne a Jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya.

Rundunar ƴansandan jihar, ta bakin kwamishinanta, Ibrahim Adamu Bakori, wadda ta tabbatar da aukuwar lamarin, ta ce ya faru ne akan bypass na Mariri dake yammacin birnin Kano.

Rahotanni sun ce jami’an ƴansanda da na hukumar agajin gaggawa sun garzayar wurin da aka samu fashewar domin kai ɗauki, a yayin da lamarin ya haddasa ruɗani da firgici a zukatan al’ummar yankin.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ya ce fashewar na iya kasancewa bam ɗin da sojoji suke jigilarsa ne wanda aka yi sakaci ya fashe.

Binciken farko-farko ya nuna cewa abin fashewar na cikin wata babbar mota ce, wadda ta ɗauko kaya, mallakain wasu masu sana’ar gwangwan, kuma take kan hanyar zuwa Jihar Yobe.

Rundunar ƴansandan Kanon ta ce ta gani wasu ƙakkrin abubuwan fashewa da ba su kai ga tashi ba a inda lamarin ya faru, kuma  tana  cigaba da bincike akan yadda aka samo su.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa'adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDPAIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da ZamfaraSojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta'addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a SokotoCOAS Shaibu ya yi Kira da a Haɗa Kai Yayin da Sojoji Ke Faɗaɗa Zuwa Rukunoni 12Najeriya ta Shirya Horarwa ta Yankuna Kan Gano da Bin Diddigin Ƙananan MakamaiSojoji Sun Kai Harin Sama da ya Hallaka Ƴan ISWAP Sama da 40, ya Lalata Motoci a BornoAmurka ta Zargi Najeriya da Daukar Yara Sojoji, Masana'antun Jarirai da Fataucin MutaneHaɗaka DMI da TMS a London ta Tsara Sabuwar Hanyar Goyon Bayan Tinubu Zuwa 2027Yushau Shuaib @57: Bikin Jagora Wanda ya Buɗe Kofofi da Canza Rayuka Daga Hafsat Ibrahim Yusha'u Shuaib @57: Barka da zagayowar Ranar Haihuwa ga Jagoran Mazaje, Mutumin da Ya Bani Dama Daga Ozumi AbdulHarin Jirgin Sama a Filin Jirgin Saudiyya ya yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 12, Raunata 309Trump ya yi Kira ga Sabon Shugaban Ukraine, ya Zargi Zelensky da Kin Amincewa da Yarjejeniyar Zaman LafiyaAFRI-CIRD ta yi Kira ga Gwamnatoci su Kara Kudin Ilimin Ƴa'ya MataAmnesty International ta yi Allah Wadai da Toshe Taron 'Dole Tinubu Ya Tafi' da Ƴan Sanda Suka yi a KanoTMG vs TMS: Matsalar Sadarwa Kan Makomar Tinubu Daga Yushau A. Shuiba 
X whatsapp