Aƙalla mutane biyar aka tabbatar sun mutu, kana wasu 15 suka jikkata sakamakon fashewar wani abu da ake zargin bam ne a Jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya.
Rundunar ƴansandan jihar, ta bakin kwamishinanta, Ibrahim Adamu Bakori, wadda ta tabbatar da aukuwar lamarin, ta ce ya faru ne akan bypass na Mariri dake yammacin birnin Kano.
Read Also:
Rahotanni sun ce jami’an ƴansanda da na hukumar agajin gaggawa sun garzayar wurin da aka samu fashewar domin kai ɗauki, a yayin da lamarin ya haddasa ruɗani da firgici a zukatan al’ummar yankin.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ya ce fashewar na iya kasancewa bam ɗin da sojoji suke jigilarsa ne wanda aka yi sakaci ya fashe.
Binciken farko-farko ya nuna cewa abin fashewar na cikin wata babbar mota ce, wadda ta ɗauko kaya, mallakain wasu masu sana’ar gwangwan, kuma take kan hanyar zuwa Jihar Yobe.
Rundunar ƴansandan Kanon ta ce ta gani wasu ƙakkrin abubuwan fashewa da ba su kai ga tashi ba a inda lamarin ya faru, kuma tana cigaba da bincike akan yadda aka samo su.