Ikirari: Wani faifen bidiyo da aka yada ta manhajar whatsapp ya nuna wasu mutane kwance da bundugu raye a wuyansu. Wanda a jikin bidiyon aka rubuta cewa, wadannan wasu ‘yan bindiga ne da suka yi garkuwa da wasu mutane ‘yan kabilar Nufe a jihar Kwara, cikin garin Lafiagi, amma cuka mutu cikin sa’oi 24 da yin garuwar.
A jikin bidiyo an yi rubutun ne kamar haka:
“Wannan lamarin ya auku ne a yankin al’ummar dake Magana da yaren Nufanci a jihar Kwara, a garin Lafiagi. An yi garkuwa da al’ummar yankin kuma aka kai su wani waje da babu wanda ya sani. Amma cikin sa’oi ashirin da hudu, kawai sai masu garkuwar suka fara mutuwa daya bayan daya, kamar yadda aka bayyana a bidiyon. A sama ga gyarren bidiyon cikin harshen nufanci.”
A bidiyon, PRNigeria ta gano abinda ake cewa cikin harshen nufanci. Bayan ta fassara ana cewa wannan masu garkuwa ne bayan su yi garkuwa da mutane sun kai su daji, da safe, suka fara mutuwa daya bayan daya, ba tare da sanin makasudin hakan ba.
Mai maganar ya kara da cewa wadanda lamarin ya rutsa da su sun fantsama cikin daji domin tsira da rayukan, don haka ya kamata mutane su taya su murna domin “Allah ya fara amsar Addu’oin su.” Ya kuma yi addu’ar kada ‘yan ta’addan su sake zuwa garin Nufawa.
Read Also:
Binciken sahihancin labara: domin tabbatar da sahihancin ikirain, PRNigeria ta gudanar da bincike kwakkwafi kan bidiyon inda ta raba shi sala-sala a manhajar “Reverse image searches”
Binciken ya nuna cewa hotunan dake cikin bidiyon ba daga jihar Kwara ya fito ba daga jihar Borno dake arewa maso gabashin Nijeriya yake.
Ya nuna mayakan Boko Haram ko ISWAP takwas da dakarun hadin gwiwa na CJTF da HF suka hallaka a garin Manawaji, dakekaramar hukumar Gamboru Ngala a jihar Borno. Sojojin sun sami nasarar hallaka mayakan bayan wani artabu da suka yi. Inda suka kwato makamai gami da alburusai.
Haka kuma wani bincike kan hotunan ya nuna shi matsayin hoton dake cikin hotunan da aka walafa a labarin nasarar da dakarun Operation Hadin kai suka samu a jihar Borno
Kammalawa: bidiyon dai na nuna hotunan mutum takwas na mayakan boko haram ko ISWAP da sojoji suka hallaka a jihar Borno bashi da wata alaka da jihar kwara.
Hukunci: ikirarin da ke cewa ‘yanbindiga sun mutum kwatsam a yankin da ake Magana da harshen Nufanci a jihar kwara bayan sun yi garkuwa da mazauna garin ba gaskiya bane, bidiyon da aka yi domin a karfafi hoton an yi shi ne da wata manufa
daga PRNigeria
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1485 days 23 hours 12 minutes 45 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1468 days 54 minutes 10 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com