Gwamnan Kano ya naɗa sabon shugaban ma’aikatan fadar Gwamnatin jihar

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya nada Dr. Sulaiman Wali a matsayin sabon shugaban ma’aikatan fadar Gwamnatin .

Hakan ma kunshe ta cikin wata sanarwa da Daraktan yada Labaran Gwamnan Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar

Dr. Wali kwararre likita Kuma ya taba zama babban sakataren a fadar Gwamnatin Kano.

Kafin wannan mukamin Dr. Wali ya kasance mai nawa gmwann kano shawara kan harkokin ma’aikata.

Hakazalika Wali ya taba rike Shugaban asibitin kwararru na Murtala muhammad da na asibitin Abdullahi wase

Har ila yau Sanarwar ta ce Gwamna Abba ya Kuma amince da nadin manjo janar Muhammad Sani a matsayin babban Daraktan ayyuka na musamman a gidan Gwamnati

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com