Sojojin Najeriya – ƙarƙashin rundunar ‘Operation Hadin Kai’ mai yaƙi da ta’addanci – sun kashe mayaƙan Boko Haram 24 a wani mummunan hari da suka ƙaddamar kan maɓoyarsu a yankin raewa maso gabashin Najeriya.
Mataimakin dakartan hulda da jama’a na rundunar, Captain Reuben Kovangiya ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar.
Read Also:
Captain Kovangiya ya ce cikin wadanda aka kashe har da mutum biyar da ke samar wa mayaƙan makamai, waɗanda aka yi wa kwanton-ɓauna a wani samame da sojojin suka ƙadamar cikin dare.
Sanarwar ta ce sojojin sun ƙaddamar hare-haren ne dajin Sambisa da yankin Timbuktu da tsaunukan Mandara da wasu wurare, tun daga ranar 4 zuwa 9 ga watan da muke ciki.
Sojojin sun kuma samu nasarar ƙwato makamai da alburusai da wasu kayyakin yaƙin ƙungiyar ta Boko Haram.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1484 days 2 hours 42 minutes 27 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1466 days 4 hours 23 minutes 52 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com