Yadda Jami’an tsaro suka kama ni -Danbello

Rahotannin sun tabbatar da cewa jami’an tsaro a Nigeria sun kama Mai Wasan barkwancinan a shafukan sada zumunta Dr. Bello Habib Galadanci wanda aka fi Sani da Danbello.

Danbello dai ya jima ya yin wasanni barkwanci inda a ciki yake nuna yadda Shugabanni a Nijeriya suka Gaza yiwa talakawan Kasar abubuwan da suka dace.

An dai kama Danbello ne a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano dake Kano , Jim kadan bayan saukarsa daga jirgin sama .

Dama dai Danbello yana zaune ne a Kasar China inda daga chan yake yin duk abun da yake yi .

Ana zargin Jami’an tsaron da suka kama Danbellon sun zo ne daga Abuja.

Sai dai duk da cewa ba a bayyana dililin kama Danbello ba, Amma mintoci kadan bayan kama shin kuma aka sake shi .

A wata hirarsa da manema labarai Danbello ya ce ” Bayan sakkowarmu daga jirgi sai wasu mutane masu kama da Jami’an tsaro suka karbi Fasfo dina da sauran takarduna , kuma suka ce In shiga wata mota”.

” Ana haka sai ga Barr. Abba Hakima nan sai akai Dan yi waya sannan akai dogon turanci bayan awa daya sai suka sallameni, Amma dama ban yi mamakin kamani ba, don dama da Shirin hakan na zo.

Tuni dai Danbello yana cikin Iyalansa bayan sakinsa da Jami’an tsaron suka yi.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1486 days 6 hours 35 minutes 51 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1468 days 8 hours 17 minutes 16 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com