Tsohon shugaban mulkin soji a Najeriya Janar Ibrahim Babangida ya miƙa ta’aziyarsa bisa rasuwar tsohon shugaban ƙasar, Muhammadu Buhari inda ya bayyana shi da mutum mai kyawawan halaye, kuma mai kishin ƙasa.
IBB wanda ya hamɓarar da Buhari daga mulkin soji a ranar 27 ga watan Agustan 1985, ya bayyana shi a matsayin mutumin da ko bayan barinsa mulki, ya cigaba da kasance abin koyi ga mutane da dama kuma abin misali.
Ya kuma tuna lokacin da ya fara haɗuwa da marigayi Buhari a shekarar 1962 a lokacin da suka shiga makarantar horar da sojoji da ke Kaduna.
Read Also:
“Tun a lokacin Muhammadu Buhari mutum ne na daban, bai cika magana ba, amma yana da jajircewa, kuma mutum ne mai bin ƙa’ida kuma mai sauƙin kai, mai tsananin kishin ƙasa ne da sadaukar da kai ga Najeriya. A cikin shekarun, mun kasance tare cikin wahala da daɗi da jarabawa da kuma cin nasara da rashinsa.”
Babangida ya ce duk da shi da Buhari sukan saɓa kan wasu abubuwa, kamar yadda a kan samu tsakanin ƴanuwa, “amma ko kaɗan ban taɓa kokwanto game da gaskiyarsa da kishin ƙasa ba.
”Bayan aiki kuma na san shi a matsayin mutum mai addini wanda kuma ke tafiyar da rayuwarsa cikin tawali’u.” in ji tsohon shugaban mulkin sojin.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1487 days 20 hours 41 minutes 28 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1469 days 22 hours 22 minutes 53 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com