Mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya miƙa ta’aziyyarsa bisa rasuwar tsohon maigidansa, Muhammadu Buhari.
Osinbajo ya kasance abokin takarar Buhari a zaɓukan shugaban ƙasa na 2015 da 2019, kuma ya yi aiki a matsayin mataimakin shugaban kasa tare da Buhari na shekara takwas.
A saƙon ta’aziyyar da ya aike, tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya wallafa cewa : ”Ni da mai dakina Dolapo mun sami labarin rasuwar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da rana”
Read Also:
Ya kuma ce ya yi magana da Aisha Buhari, matar tsohon shugaban ƙasar, da kuma ɗansa Yusuf Buhari domin miƙa ta’aziyyarsa da kuma taya su alhinin rashinsa, wanda a cewarsa yana alfahari da aiki tare da shi na tsawon shekara 8 da ba zai taɓa mantawa dasu ba.
Mista Osinbajo ya ce Najeriya ta yi asarar mai ƙishin ƙasa na asali, wanda rayuwarsa ta kasance cike da ayyukan da ke nuna sadaukarwa ga ƙasarsa da yake ƙauna.
” Tarihin Buhari zai bayar da shaida game da martaba aikin gwamnati da ke cike da gaskiya, da kuma sadaukarwa ga cigaban alumma,” in ji tsohon mataimakin shugaban ƙasar.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1488 days 57 minutes 9 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1470 days 2 hours 38 minutes 34 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com