Fitaccen ɗan siyasa kuma tsohon gogaggen ɗanjaridar nan na Najeriya, Dele Momodu ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar PDP zuwa sabuwar haɗakar ADC ta ‘yan hamayya.
Momodu – wanda ya taɓa tsayawa takarar shugaban ƙasar – ya ce ya ɗauki matakin ne saboda yadda wasu da ya kira ”masu yaƙi da dimokraɗiyya” suka hana jam’iyyar numfashi.
Read Also:
Cikin wasiƙar ficewar tasa da ya aike wa shugaban jam’iyyar na mazaɓarsa ta Ihievbe a ƙaramar hukumar Owan ta Gabas, ranar Alhamis 17 ga watan Yuli, fitaccen ɗansiyasar ya ce dole ce ta sa ya ɗauki matakin domin maido da martabar dimokraɗiyya.
“Dalilina a bayyane yake, wasu masu yaƙi da dimokraɗiyya sun maƙure jam’iyyar daga ciki da wajen jam’iyyar”, kamar yadda wani sashe na wasiƙar ya nuna.