EFCC ta kama ƴan damfara ta intanet 25 a Jami’ar Bayero dake Kano

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Najeriya (EFCC) ta kama wasu mutum 25 da ake zargi da aikata damfara ta intanet a wani samame da ta kai a harabar jami’ar Bayero da ke Kano.

Hukumar ta ce jami’anta sun gudanar da samamen ne bisa sahihan bayanan sirri da suka samu da ke nuna cewa mutanen na da hannu a ayyukan damfara ta intanet da kuma satar bayanan mutane.

Hukumar ce ta sanar da hakan a shafin sada zumuntanta na X. inda ta ce dukkan waɗanda aka kama dalibai ne na jami’ar, kuma an gano wayoyi da kwamfutoci da mota kirar Honda Accord a hannunsu.

Kayan da aka kwato daga wurin sun haɗa da wayoyin salula, kwamfutoci, na’urorin haɗi da mota kirar Honda Accord.

EFCC ta ce an kama su ne bayan makonni ana sa ido a kansu kuma za a gurfanar da su a kotu da zarar an kammala bincike.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com