Home Labarai NAFDAC ta gano gidan ajiye sinadaran haɗa abubuwa masu fashewa a Kano

NAFDAC ta gano gidan ajiye sinadaran haɗa abubuwa masu fashewa a Kano

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta ƙasa (NAFDAC) ta gano wani babban gidan ajiya a Kano da ke cike da sinadarai masu haɗari da ake amfani da su wajen haɗa abubuwa masu fashewa, ciki har da sinadarin sulphuric da nitric acid kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

cewar hukumar, an gano lita 60,000 na sulphuric acid da kuma lita 28,560 na nitric acid da kuma jarkoki da suka kai 330 da aka riga aka fitar da sinadaran cikinsu ba tare da sanin inda aka kai su ba a cikin gidan.

“Abin da muka gani a nan ya girgiza mu. Ban taɓa ganin adadin waɗannan sinadarai masu haɗari a wuri guda ba,” in ji Farfesa Adeyeye.

Hukumar ta ce ba a samu wandan yake da gidan ajiyar ba a lokacin da aka isa wurin, amma an kama wani ma’aikacin da ke kula da wurin, kuma ana ci gaba da bincike don gano wanda yake da wurin da kuma inda ya samo sinadaran da kuma inda yake kai su.

NAFDAC ta bayyana cewa sinadaran na cikin jerin kayan da ke da haɗari sosai ga mutane saboda haka sai da izini daga ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro kafin a shigo da su ƙasar.

Hukumar ta kuma tabbatar da cewa za ta lalata sinadaran bisa ka’idojin da suka dace don kare lafiyar jama’a, sannan za ta tabbatar da cewa an gurfanar da wanda ya mallaki sinadaran a gaban shari’a.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
HOTO: NSCDC ta Tsare Jami'ai 24 Kan Mutuwar Masu Hakar Ma'adinai a TsareShirin Tallafin Mai: Atiku ya yi Watsi da Gaskiyar Magana – APCGwamnatin Tarayya ta Inganta Samar da Abinci ta Hanyar Shirin AgriShield na ONSA Daga Chido OnumahAtiku ya yi Tambaya Kan Rashin Zuwa UNGA a Karo na Uku da Tinubu ya yi, ya Nemi Karin BayaniFalconets ta Fice Daga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata Ƴan Kasa da Shekaru 20 Bayan Colombia ta Sha Kashi a Wasan KarsheMatawalle Ya Nemi Tallafin Czech Don Samar da Alburusan DICON da Canja FasahaRundunar Sojojin Najeriya Ta Tallafa wa Iyalan Sojojin Gambia da Suka MutuFilato: Sojoji Sun Kama Masu Garkuwa 11, Sun Kwato MakamaiOPHK ta yi Bayani Kan Rahoton Amnesty na 2016 Dangane da Mutuwar da Ake Zargi a Barkin Giwa2027: Sama da Mambobin Jam'iyyar NDC 6,000 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a EnuguKwankwaso ya Nuna Aniyar Yin Sulhu da Gwamna YusufYadda Hon. Hudu Kanje Ya Sake Fasalin Jagorancin Cigaban Kasa Daga Mika'il Ja'afarƳan Sanda Sun Kama Mutane 300 a Farmakin Wuraren da Ake Aikata Laifuka a FCT Sun Kwace Wukake, Bindigar Wasa, da WiwiZakari Mohammed: Dole Kwara ta Cika Kwarewarta – Dan Takarar ADC ya Nemi Muhawara a BayyaneWSCIJ ta Yaba wa PRNigeria Kan Ci Gaba da Tallafawa Matasa Wajen Sadarwa Bayan Karewar Tallafi
X whatsapp