Home General Gwamnatin jihar Zamfara ta tabbatar da rasuwar Sarkin Gusau na jihar

Gwamnatin jihar Zamfara ta tabbatar da rasuwar Sarkin Gusau na jihar

Gwamnatin jihar Zamfara ta tabbatar da mutuwar sarki na 16 a jerin sakarakunan Gusau  mai Martaba Dr. Ibrahim Bello.

wannan dai na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan Jihar Sulaiman Idris Ya fitar tare da bayyana jimamin Gwamnatin jihar bisa wannan babban rashi.

sanarwar ta kuma bayyana kaduwar gwamnan jihar Dauda lawan, wanda ya  bayyana marigayi sarkin matsayin babban uba kuma shugaba mai kishin ci gaban jihar Zamfara.

“Ina matuƙar alhini da jin labarin rasuwar mahaifinmu, Mai Martaba Sarkin Gusau, Dr. Ibrahim Bello.” in ji sanarwar.

“Ina mika ta’aziyya ta ga majalisar sarakunan jihar da iyalan marigayin da masarautar Gusau da kuma ɗaukacin al’ummar jihar Zamfara.” gwamnan ya cewa.

Sarkin dai ya rasu a ranar Juma’a yana da shekaru 71, bayan fama da doguwar jinya a birnin Abuja, wanda shi ne sarki na 16 a jerin sarakunan Gusau, kuma ya gaji mahaifinsa da ya rasu a ranar 16 ga Maris, 2015.

Marigayin ya shafe shekaru 10 da wasu watanni yana kan karagar mulki. daga bisani sanarwa bayyana cewa za’a yi Jana’iza sa a yau juma a garin Gusua

Daga PRNigeria

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa'adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDPAIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da ZamfaraSojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta'addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a SokotoCOAS Shaibu ya yi Kira da a Haɗa Kai Yayin da Sojoji Ke Faɗaɗa Zuwa Rukunoni 12Najeriya ta Shirya Horarwa ta Yankuna Kan Gano da Bin Diddigin Ƙananan MakamaiSojoji Sun Kai Harin Sama da ya Hallaka Ƴan ISWAP Sama da 40, ya Lalata Motoci a BornoAmurka ta Zargi Najeriya da Daukar Yara Sojoji, Masana'antun Jarirai da Fataucin MutaneHaɗaka DMI da TMS a London ta Tsara Sabuwar Hanyar Goyon Bayan Tinubu Zuwa 2027Yushau Shuaib @57: Bikin Jagora Wanda ya Buɗe Kofofi da Canza Rayuka Daga Hafsat Ibrahim Yusha'u Shuaib @57: Barka da zagayowar Ranar Haihuwa ga Jagoran Mazaje, Mutumin da Ya Bani Dama Daga Ozumi AbdulHarin Jirgin Sama a Filin Jirgin Saudiyya ya yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 12, Raunata 309Trump ya yi Kira ga Sabon Shugaban Ukraine, ya Zargi Zelensky da Kin Amincewa da Yarjejeniyar Zaman LafiyaAFRI-CIRD ta yi Kira ga Gwamnatoci su Kara Kudin Ilimin Ƴa'ya MataAmnesty International ta yi Allah Wadai da Toshe Taron 'Dole Tinubu Ya Tafi' da Ƴan Sanda Suka yi a KanoTMG vs TMS: Matsalar Sadarwa Kan Makomar Tinubu Daga Yushau A. Shuiba 
X whatsapp