Fadar shugaban Kasa ta magantu kan zargin da Kwankwaso ya yiwa Tinubu

Fadar Shugaban Ƙasa ta musanta zargin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso cewa gwamnatin Bola Tinubu ta watsar da yankin Arewa, tana mai cewa arewacin Najeriya na samun gagarumin kulawa a ayyukan ci gaba.
Kwankwaso, a wani taron tattaunawa kan gyaran kundin tsarin mulki da aka gudanar a Kano, ya soki gwamnatin Tinubu da karkatar da albarkatun ƙasa zuwa kudu, yana mai cewa hakan na ƙara jefa Arewa cikin fatara da rashin tsaro. Ya kuma koka da halin da titunan tarayya ke ciki a yankin, inda ya bada misalin wata tafiyarsa daga Abuja zuwa Kano da ya kira da “azaba” sakamakon lalacewar hanya.
Sai dai da yake mayar da martani, mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Sunday Dare, ya ce kalaman Kwankwaso sun saba wa gaskiya, domin gwamnatin Tinubu na aiwatar da manyan ayyuka a Arewa da suka shafi hanyoyi, noma, lafiya da makamashi.
Ya lissafa muhimman ayyuka kamar titin Abuja–Kaduna–Kano, bututun iskar gas na Ajaokuta–Kaduna–Kano, shirin noma a jihohi tara, da aikin Kolmani a Bauchi da Gombe. Ya kuma ce an farfaɗo da cibiyoyin lafiya 1,000 a Arewa tare da bunƙasa wasu asibitoci manya.
Dare ya ƙara da cewa duk waɗannan nasarori an cimma su ne a cikin shekaru biyu kacal da Shugaba Tinubu ya hau mulki, yana mai cewa Arewa na da muhimmiyar matsayi a tsarin ci gaban gwamnatin.
 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com