Gwamnatin jihar Zamfara ta tabbatar da mutuwar sarki na 16 a jerin sakarakunan Gusau mai Martaba Dr. Ibrahim Bello.
wannan dai na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan Jihar Sulaiman Idris Ya fitar tare da bayyana jimamin Gwamnatin jihar bisa wannan babban rashi.
sanarwar ta kuma bayyana kaduwar gwamnan jihar Dauda lawan, wanda ya bayyana marigayi sarkin matsayin babban uba kuma shugaba mai kishin ci gaban jihar Zamfara.
“Ina matuƙar alhini da jin labarin rasuwar mahaifinmu, Mai Martaba Sarkin Gusau, Dr. Ibrahim Bello.” in ji sanarwar.
Read Also:
“Ina mika ta’aziyya ta ga majalisar sarakunan jihar da iyalan marigayin da masarautar Gusau da kuma ɗaukacin al’ummar jihar Zamfara.” gwamnan ya cewa.
Sarkin dai ya rasu a ranar Juma’a yana da shekaru 71, bayan fama da doguwar jinya a birnin Abuja, wanda shi ne sarki na 16 a jerin sarakunan Gusau, kuma ya gaji mahaifinsa da ya rasu a ranar 16 ga Maris, 2015.
Marigayin ya shafe shekaru 10 da wasu watanni yana kan karagar mulki. daga bisani sanarwa bayyana cewa za’a yi Jana’iza sa a yau juma a garin Gusua
Daga PRNigeria
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1499 days 19 hours 1 minute 6 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1481 days 20 hours 42 minutes 31 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com