Akalla mutum 14 da wani ɗan sanda na MOPOL ne suka mutu a hare-hare biyu da wasu ‘yan bindiga suka kai a ƙaramar hukumar Bokkos da ke Jihar Filato a ranar Alhamis, 24 ga Yuli, 2025.
Rahotanni sun ce an kai ɗaya daga cikin hare-haren ne da misalin ƙarfe 4 na yamma, yayin da mutanen da lamarin ya shafa mafi yawansu daga ƙauyen Chirang ke dawowa daga kasuwar Bokkos zuwa ƙauyen Mangor.
Shugaban masu sa ido kan zaman lafiya na ƙaramar hukumar Bokkos, Kefas Mallai ne ya tabbatar da faruwar lamarin ga jaridar Punch inda ya ce mutane 14 ne suka mutu, yayin da wasu uku kuma suka jikkata.
A cewar Mallai, kafin wannan harin, wasu ‘yan bindiga sun harbe wani ɗan sandan MOPOL a wani shingen bincike da ke hanyar Richa a safiyar ranar.
Shugaban ƙaramar hukumar Bokkos, Amalau Amalau, ya bayyana lamarin a matsayin “taƙaici da ke buƙatar ɗaukar matakin gaggawa,” yana mai cewa an riga an kai gawarwaki da waɗanda suka jikkata zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Alabo Alfred, bai samu damar bayyana komai ba a lokacin da aka nemi jin ta bakinsa.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1499 days 11 hours 53 minutes 32 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1481 days 13 hours 34 minutes 57 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com