Akalla jami’an tsaron jihar Katsina 100 suka mutu a bakin aiki – Kwamishina

Gwamnatin Jihar Katsina dake Najeriya ta ce akalla jami’an tsaron ta sama da 100 suka mutu a ci gaba da aikin da suke na karkaɗe ƴanta’addan da suka hana jihar zaman lafiya.

Kwamishinan tsaro na jihar Nasir Mua’zu ya sanar da haka, inda ya ce baya ga ƴansanda sama da 30 da aka kashe, akwai kuma wasu sojojin da suka mutu yayin aikin kare lafiya da dukiyoyin jama’ar jihar.

Mua’zu wanda ke mayar da martani a kan wasu rahotanni a kafofin sada zumunta da ya ce ana amfani da su domin tada hankalin jama’a, ya ce gwamnan jihar na iya bakin koƙarinsa wajen ganin ya tinkari wannan matsala ta ƴanta’adda wadda sannu a hankali ya ce su na samun nasara a kan ta.

Kwamishinan ya ce lokacin da Gwamna Dikko Radda ya karbi ragamar tafiyar da jihar Katsina, akalla ƙananan hukumomi 24 ke fama da matsalar ƴan ta’adda, amma kuma sakamakon haɗin kai da jami’an tsaro da kuma ƙirƙiro ƙungiyar Ƴansakai ta jihar, an yi nasarar magance ta a ƙananan hukumomi 11, yayin da matsalar kuma tayi sauki a wasu ƙananan hukumomi guda 9.

Mua’zu ya ce ƙananan hukumomi 4 da ake ci gaba da fuskantar hare hare su ne Faskari da Ƙankara da Safana da kuma Matazu, amma hakan ba ya na nuna cewa sun gaza ba ne, domin jami’an tsaro na iya bakin ƙoƙarin su wajen tabbatar da zaman lafiya a wuraren.

Kwamishinan ya ce duk da hadarin da ya yi kwanakin baya, gwamnan bai daina tattaunawa da masu ruwa da tsaki a harkar tsaro ba, da kuma manyan hafsoshin tsaron dake jihar, domin ganin an kare lafiya da dukiyoyin jama’a.

Mua’zu ya buƙaci goyan baya daga kowanne bangare, maimakon sukar irin matakan da suke ɗauka a kan wannan matsalar dake hana su bacci, musamman ganin yadda jami’an tsaron ke sadaukar da rayukansu wajen kare lafiya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com