Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa a Arewa Maso yammacin Nijeriya ta tabbatar da mutuwar mutane 7 cikin su har da kananan yara sakamakon hadarin jirgin ruwa a karamar hukumar Taura dake jihar.
Wannan na cikin wata sanarwa da kakakin rundunar SP Shi’isu Lawan Adam, Anipr, ya aikewa PRNigeria a yammacin ranar talata, inda ya ce rundunar ta nuna bakin cikin ta bisa aukuwar hadarin da ya rutsa da matafiya a kauyen Zangwan Maje dake karamar hukumar ta Taura.
Read Also:
Sanarwa ta ce a ranar 27 ga watan Yunin 2025, rundunar ta sami wani kiran gaggawa da ke cewa a kalla yara 15 dake kan hanyarsu ta dawowa daga gona a Jejin Gunka zuwa kauyen Zangwan Maje jirgin da suke ciki ya kife bisa Ambaliyar ruwa da iska mai karfi da kuma lodin da suka yiwa jirgin ya wuce kima.
Sai dai bayan daukin gaggawa da aka kai musu an sami nasarar kubutar da yara 7 a raye, yayin da aka sami nasarar gano gawarwakin yara 2 dukkanninsu mata, haka nan kuma a safiyar talata an sami nasarar gano gawarwakin yara mata 4.
Tuni dai likitoci suka tabbatar da mutuwar yaran kamar yadda sanarwar ta tabbatar.
Kwamishinan ‘yansandan jihar CP, Dahiru Muhammad, psc, fdc ya mika ta’aziyyarsa ga iyalai da ‘yan uwan wadanda hadarin ya rutsa da su da ma daukacin al’ummar kauyen Zangwan Maje.
Ya kuma yi kira ga mazauna yankin da su kaucewa yin tafiyar dare, tare da gujewa daukar kayan da suka wuce kima, su kuma ringumi yin amfani da rigar ruwa a dukkan lokacin da za su shiga jirgin ruwa.
Daga PRNigeria