Wasu Rahotannin sun bayyana cewa zanga-zanga ta ɓarke a daya daga cikin manyan sansanonin ‘yan gudun hijira na Kenya a ranar Litinin, inda aka samu rahoton mutuwar mutum ɗaya da jikkatar wasu, bayan watanni da aka shafe ana tankiya saboda katsewar agaji.
Sansanin ‘yan gudun hijira na Kakuma, da ke arewacin Kenya, shine na biyu mafi girma a ƙasar, kuma yana ɗaukar ‘yan gudun hijira kusan 300,000 daga Sudan ta Kudu da Somalia da Uganda da kuma Burundi.
Read Also:
Ƙungiyoyin agaji sun sha fama da tankiya tsawon watanni bayan katse tallafin da Amurka da sauran masu ba da agaji suka yi.
Wata majiya daga ma’aikatar kula da ‘yan gudun hijira ta shaida wa kamfanin dillacin labarai na AFP cewa, Mutum ɗaya ya mutu, kuma wasu jami’an ‘yan sanda biyu sun jikkata, yana mai cewa an samu karuwar matsin lamba kan tsarin tallafin.
Duk da haka, kakakin ‘yan sanda ƙasar Michael Muchiri ya tabbatar da kasancewar jami’an a wajen rikicin amma ya ce babu wanda ya rasa ransa.
Ya ce matakin da gwamnatin Amurka ta ɗauka na katse tallafin USAID ya fara yin tasiri a kan halin da ‘yan gudun hijira ke ciki.