Home General Hadarin jirgin ruwa yayi sanadin mutuwar mutum 6 a jihar Jigawa

Hadarin jirgin ruwa yayi sanadin mutuwar mutum 6 a jihar Jigawa

Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa a Arewa Maso yammacin Nijeriya ta tabbatar da mutuwar mutane 7 cikin su har da kananan yara sakamakon hadarin jirgin ruwa a karamar hukumar Taura dake jihar.

Wannan na cikin wata sanarwa da kakakin rundunar SP Shi’isu Lawan Adam, Anipr, ya aikewa PRNigeria a yammacin ranar talata, inda ya ce  rundunar ta nuna bakin cikin ta bisa aukuwar hadarin da ya rutsa da matafiya a kauyen Zangwan Maje dake karamar hukumar ta Taura.

Sanarwa ta ce a ranar 27 ga watan Yunin 2025, rundunar ta sami wani kiran gaggawa da ke cewa a kalla yara 15 dake kan hanyarsu ta dawowa daga gona a Jejin Gunka zuwa kauyen Zangwan Maje jirgin da suke ciki ya kife bisa Ambaliyar ruwa da iska mai karfi da kuma lodin da suka yiwa jirgin ya wuce kima.

Sai dai bayan daukin gaggawa da aka kai musu an sami nasarar kubutar da yara 7 a raye, yayin da aka sami nasarar gano gawarwakin yara 2 dukkanninsu mata, haka nan kuma a safiyar talata an sami nasarar gano gawarwakin yara mata 4.

Tuni dai likitoci suka tabbatar da mutuwar yaran kamar yadda sanarwar ta tabbatar.

Kwamishinan ‘yansandan jihar CP, Dahiru Muhammad, psc, fdc ya mika ta’aziyyarsa ga iyalai da ‘yan uwan wadanda hadarin ya rutsa da su da ma daukacin al’ummar kauyen Zangwan Maje.

Ya kuma yi kira ga mazauna yankin da su kaucewa yin tafiyar dare, tare da gujewa daukar kayan da suka wuce kima, su kuma ringumi yin amfani da rigar ruwa a dukkan lokacin da za su shiga jirgin ruwa.

Daga PRNigeria

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa'adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDPAIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da ZamfaraSojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta'addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a SokotoCOAS Shaibu ya yi Kira da a Haɗa Kai Yayin da Sojoji Ke Faɗaɗa Zuwa Rukunoni 12Najeriya ta Shirya Horarwa ta Yankuna Kan Gano da Bin Diddigin Ƙananan MakamaiSojoji Sun Kai Harin Sama da ya Hallaka Ƴan ISWAP Sama da 40, ya Lalata Motoci a BornoAmurka ta Zargi Najeriya da Daukar Yara Sojoji, Masana'antun Jarirai da Fataucin MutaneHaɗaka DMI da TMS a London ta Tsara Sabuwar Hanyar Goyon Bayan Tinubu Zuwa 2027Yushau Shuaib @57: Bikin Jagora Wanda ya Buɗe Kofofi da Canza Rayuka Daga Hafsat Ibrahim Yusha'u Shuaib @57: Barka da zagayowar Ranar Haihuwa ga Jagoran Mazaje, Mutumin da Ya Bani Dama Daga Ozumi AbdulHarin Jirgin Sama a Filin Jirgin Saudiyya ya yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 12, Raunata 309Trump ya yi Kira ga Sabon Shugaban Ukraine, ya Zargi Zelensky da Kin Amincewa da Yarjejeniyar Zaman LafiyaAFRI-CIRD ta yi Kira ga Gwamnatoci su Kara Kudin Ilimin Ƴa'ya MataAmnesty International ta yi Allah Wadai da Toshe Taron 'Dole Tinubu Ya Tafi' da Ƴan Sanda Suka yi a KanoTMG vs TMS: Matsalar Sadarwa Kan Makomar Tinubu Daga Yushau A. Shuiba 
X whatsapp