Gini kan magudanan ruwa ne ya haifar da Ambaliyar Maiduguri

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya NEMA ta ce mamakon ruwan sama da yin gine-gine kan magunan ruwa ne ya janyo ambaliyar Maiduguri.

A ranar Laraba ne aka samu rahotonni ambaliya a wasu unguwannin birnin Maiduguri da yankin ƙaramar hukumar Jere sakamakon ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da aka shafe tsawo sa’a uku ana tafkawa a birnin.

Cikin wata sanarwa da shugaban hukumar NEMA, Zubaida Umar ta wallafa a shafinta na Facebook ta danganta ambaliyar da rashin bin tsarin gine-gine.

”ambaliyar na da alaƙa da mamakon ruwan sama da aka samu a birnin da kuma rashin kula da kwalbatoci da yin gine-gine kan hanyoyin da ruwa ke bi”, in ji shugabar ta NEMA.

Hukumar ta NEMA ta ce jami’anta tare da haɗin gwiwar sauran hukumomi sun taimaka wajen ceto mutanen da ambaliyar ta rutsa da su tare da rage illar ambaliyar.

Ambaliyar na zuwa ne ƙasa da shekara guda bayan wata mummunar ambaliyar da ta auka wa yankin, wadda ta yi sanadiyyar raba fiye da mutum miliyan guda da muhallansu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com