KACHMA ta yabawa KAROTA bisa inganta lafiyar Jami’anta

Hukumar Kula da zirga-zirgar ababawan hawa ta jihar Kano (KAROTA) na shirin yin hadin gwiwa da KACHMA don inganta lafiyar ma’aikatanta

Wannan na cikin wata sanarwa da Jami’in Hulda da Jama’a  na hukumar Abubakar Ibrahim Sharada ya fitar ya kuma aikewa PRNigeria wadda ta cewa, Manajan Daraktan Hukumar Hon. Injiniya Faisal Mahmud Kabir ne ya bayyana aniyar hukumar na yin hadin gwiwar yayin da yake karbar bakuncin sakatariyar zartawar hukumar ta (KACHMA) Dr Rahila Muktar a shalkwatar hukumar karota.

Hon. Faisal Mahmud ya bayyana cewa lafiyar ma’aikatan KAROTA na daga cikin abubuwan da yake baiwa muhimmanci sosai, ganin irin hadurran da ke tattare da ayyukan da suke gudanarwa.

Shugaban KAROTA ya bayyana cewa hukumar na da shirin gyara da fadada asibitin ma’aikatan da ke cikin hukumar domin ya kai ga ingantaccen mataki na aiki.

Ya yaba wa Sakatariyar Zartarwa ta KACHMA bisa wannan ziyara, inda ya tabbatar da cewa za a samu kyakkyawar hulɗa wacce za ta haifar da sakamako mai amfani.

Tun da farko, Dr Rahila Muktar ta bayyana cewa ziyararta KAROTA na da nufin kawo gudunmawar kiwon lafiya daga KACHMA har gida ga ma’aikatan hukumar.

haka kuma ta nuna jin daɗinta bisa kokarin da shugabannin KAROTA suka yi wajen samar da kayayyakin kiwon lafiya a asibitin ma’aikatan su.

Dr Rahila ta tabbatar da cewa KACHMA za ta ba da goyon baya wajen tallafa wa asibitin KAROTA domin ya kai wani mataki na ci gaba da inganci.

PRNigeria

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com