Babbar jam’iyyar adawa a Najeriya PDP na shirin kaddamar da kwamitocin zartaswa na shiyoyi da kuma kwamitin tsara zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyar na shekarar 2027 a ranar Alhamis a Abuja.
Wannan na zuwa ne yayin da ake samun rabuwar kawuna tsakanin mambobin kwamitin zartaswa na ƙasa na jam’iyar wato NEC kan yunƙurin dawo da tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan da kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour a 2023, Peter Obi, cikin jam’iyyar.
Wasu daga cikin shugabannin PDP na ganin cewa Jonathan ya bar jam’iyyar a lokaci mai muhimmanci, yayin da Obi kuma ya yi sauya sheƙa zuwa Labour, lamarin da ya rage wa jam’iyyar damar samun nasara a zaɓen 2023.
Sai dai wasu mambobin kwamitin zartaswar sun yi maraba da wannan yunƙuri, suna cewa PDP na da isassun jiga-jigai masu kwarewa waɗanda za su iya wakiltar jam’iyyar a zaɓen 2027.
Rahotanni sun tabbatar da cewa jam’iyyar ba ta kai ga tuntuɓar Jonathan da Obi a hukumance ba, sai dai wasu mutane ne daban-daban ke yin hakan a madadinta.
Kakakin jam’iyyar PDP na ƙasa, Debo Ologunagba, ya ce ƙaddamar da kwamitin zartarwar zai gudana ne a ranar Alhamis, tare da jaddada cewa jam’iyyar na da wadatattun masu neman takarar shugabanci a cikinta.