Ƙungiyoyin ma’aikatan manyan makarantun Najeriya na ci gaba da yin watsi da sabon shirin da gwamnatin tarayyar kasar ta ɓullo da shi domin inganta jin dadin ma’aikata, da haɓaka ƙwarewar aiki, ga ma’aikatan manyan makarantun ƙasar.
Ita dai gwamnatin Najeriyan ta ƙaddamar da wani sabon shiri wanda aka tsara zai bayar da bashin kudi har naira miliyan 10 ga ma’aikatan manyan makarantun ƙasar da suka haɗa da na jami’a da kwalejin kimiyya da fasaha da kuma kwalejin ilimi.
To sai dai ƙungiyoyin ma’aikatan na ganin cewa ba hanyoyin samar da bashi gare su ya kamata gwamnatin ta ɓullo da su ba a wannan lokaci da ake ciki.
Sun ce kamata ya yi gwamnatin ta mayar da hankali wajen inganta albashinsu da kuma biyan su ɗimbin basukan albashi da na alawus-alawus da suke bin ta.
Kungiyar malaman jami’o’i ta Najeriya (ASUU) na cikin masu wannan ra’ayi, kuma Farfesa Ibrahim Tajo Suraj, shugaban reshen kungiyar na Jami’ar Bayero ta Kano ya ce su ma labarin Shirin bayar da bashin kawai suka ji a jaridu, amma babu wanda ya tuntuɓe su kafin sanarwar gwamnatin.
”Abin da muke dubawa shi ne, mutum ne yada da haƙƙoƙinsa da ya ke bin ka, maimakon ka biya shi haƙƙoƙinsa sai ka ce za ka ba shi bashi.” In ji Farfesa Tajo Suraj.
Ya ƙara da cewa ”Akwai abubuwa da yawa da ya kamata a yi mana, ba a zo an yi ba na haƙƙoƙi, kawai sai ka ce za ka bamu bashi. Bashin kuma ai ba nema muka yi ba, na taɓa ba mutum bashi bai nema ba? mu kullum abin da muke cewa shi ne, in dai ka yi shi ne don ka inganta rayuwar ma’aikatan jami’oi, mai zai hana ka inganta tsarin albashinsu ba bashi ba.”
Read Also:
Farfesa Tajo Suraj ya koka da yadda tun 2009 ake ta jan ƙafa da neman kaucewa yarjejeniyar da suka ƙulla da gwamnatin Najeriya, lamarin da ya kai ga an yi wa yarjejeniyar gyaran fuska a lokuta daban-daban har ta kai an cimma matsayar amincewa da ita a bara, abin da ya rage kawai shi ne sa mata hannu ta fara aiki.
”To maimakon a sa mata hannu ta fara aiki shi ne kuma suka kawo wannan abin na kauda hankalin mutane don su nuna suna ƙoƙarin wai su inganta rayuwar malamnin jami’a.”
Malamin jami’ar ya kuma zayyana abubuwan da ƙungiyarsu ke fatan gwamnatin Najeriya ta yi wanda zai kawo mafita ga dukkan ƙorafin da suke da shi.
Ya ce kamata ya yi gwamnatin ta biya malaman haƙƙoƙinsu da ke kanta, da sake zama domin sabinta yarjejeniyar da ɓangarorin suka ƙulla tun 2009 a kuma sa mata hannu, daga nan kuma ”idan suna son bayar da bashin, to sai su bada bashinsu daga baya, wannan kuma wanda ke so sai ya je ya karɓa, amma ba yadda za ai kana bin mutum bashi, ya ƙi biyan bashin da kake binsa sai ya ce zai ba ka bashi.”
To sai dai duk da irin sukar da wannan shiri ya fuskanta daga ma’aikatan manyan makarantun Najeriya, waɗanda gwamnatin ta ce domi su ta ɓullo da shi, gwamnatin ta ƙaddamar da shirin nata, tare da bayanin irin matakai da sharuɗɗan cikawa kafin ma’aikatan manyan makarantun su ci gajiyar shirin.
Ƙaramin ministan ilimi a Najeriya Dr Tunji Alausa, ya ce sun ƙaddamar da Shirin, kuma suna sa ran ma’aikatan manyan makarantun ƙasar za su shiga domin amfana da shi.
Ya yi bayanin cewa waɗanda ke so za su iya karɓar bashin har naira miliyan 10, wanda za a rarraba yadda za su biya gwamnatin kuɗin a cikin shekaru biyar.
Dr Alausa ya ce shirin wata hanya ce ta sauƙaƙen wa ma’aikatan manyan makarantun hanyar samun kudin sayen ababen hawa da samun jarin noma da kuma damar amfani da kuɗin wajen zurfafa iliminsu.
Gwamnati da malaman manyan makarantu a Najeriya sun daɗe suna musayar kalamai da sukar juna a kan ƙoƙarin inganta tsarin ilimin, inda a lokuta da dama malaman, musamman na jami’oi ke zargin gwamnatin da nuna halin ko in kula da buƙatun gyara ilimi a ƙasar, yayin da ita kuma gwamnatin ke dagewa cewa tana bakin ƙoƙarin ta.