Wata Babbar Kotun Tarayya a Abuja babban birnin Najeriya ta bayar da umarnin dakatar da wasu asusan da ke da alaƙa da tsohon shugaban kamfanin mai na NNPCL Mele Kyari.
Kotun ta bayar da umarnin dakatar da asusan na bankin Jaiz saboda zargin zamba da kuma halasta kuɗin haram.
Mai Shari’a Emeka Nwite ne ya bayar da umarni bayan wani lauyan hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci, Ogechi Ujam, ya nemi kotun ta dakatar da amfani da asusan har zuwa lokacin da hukumar za ta kammala bincike a kansu.
“Na saurari mai ƙorafi kuma na duba takardun ƙorafin da suka shigar masu ɗauke da hujjoji da bayanai. Na lura cewa buƙatarsu ta cancanci a amince da ita,” kamar yadda alƙalin ya bayyana.
Mai Shari’a Nwite ya ɗage sauraron batun har zuwa ranar 23 ga watan Satumba domin ganin rahoton binicken.