Ya kamata kowane ɗan Najeriya ya koyi dabarar kare kai – Musa

Babban hafsan hafsoshin Najeriya, Janar Christopher Musa ya shawaraci ƴan Najeriya da su laƙanci dabarun kare kai daga haɗurra a matsayin mataki na ko-ta-kwana.

C.G Musa ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da kafar talabijin ta Channels a yau Alhamis.

Matsalar tsaro na addabar yankuna da dama na Najeriya, inda masu ɗauke da makamai ke kashe mutane tare da tarwatsa su daga muhallansu.

Duk da cewa hukumomi na cewa suna bakin ƙoƙarinsu, amma lamarin na ci gaba da laƙume ɗaruruwan rayuka a yankunan da ake fama da irin waɗannan tashin-tashina, kamar arewa maso yamma da arewa maso gabas da kuma arewa ta tsakiyar ƙasar.

Lokacin da aka tambayi Christopher Musa kan ko ya kamata al’umma su koyi dabarun faɗa, ya ce “Ya kamata mutane su ɗauki wannan tamkar koyon tuƙi ne ko iyo, wannan abu ne da ake buƙata a rayuwa, ko da ana fama da yaƙi ko a’a”.

“Ina ganin ya kamata a wayar da kan kowane ɗan Najeriya kan tsaro a kowane mataki. Kare kai na da matuƙar muhimmanci,” in ji Musa.

Ko a ranar Litinin, wasu mahara sun kashe masu ibada aƙalla 28 a wani masallaci da ke karamar hukumar Malumfashi da ke jihar Katsina, arewa maso yammacin ƙasar.

Haka nan a watan da ya gabata masu garkuwa da mutane sun yi wa mutum 38 yankan rago cikin waɗanda suke garkuwa da su a jihar Zamfara mai maƙwaftaka.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com