An fara bincike kan hatsarin jirgin ƙasa daga Abuja zuwa Kaduna

Hukumar jiragen ƙasa ta Najeriya (NRC) ta bayyana cewa an fara bincike kan hatsarin da jirgin ƙasa daga Abuja zuwa Kaduna ya yi a garin Asham dake jihar Kaduna.

Hukumar ta ce binciken zai gudana ne ƙarƙashin kulawar hukumomin da abin ya shafa tare da sa ido daga ma’aikatar sufuri ta Tarayya domin gano musabbabin lamarin.

A cikin sanarwar da NRC ta fitar a ranar Talata da yamma, ta bayyana cewa jimillar mutum 618 ne suke cikin jirgin a lokacin da ya sauka daga kan layi.

Hukumar ta ce daga cikin fasinjojin, mutum bakwai ne suka samu raunuka daban-daban kuma an garzaya da su asibiti. Sauran fasinjojin kuwa an mayar da su zuwa tashoshin Idu da Kubwa ta wani jirgi da aka tura daga Abuja.

An kuma dakatar da dukkan ayyuka da zirga-zirgar jirgin ƙasa daga Abuja zuwa Kaduna na ɗan lokaci, har sai an kammala aikin ceto da bincike da kuma gyara wurin.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com