Gwamnatin tarayya ta bayar da umarnin rufe wurin hakar maádanai ba bisa kaída ba a Gwagwalada dake birnin tarayya Abuja, domin dakile hadarin aukuwar matsalar sauyin yanayi
Ministan ma’adanai na tarayyar Nijeriya, Dele Alake, ne ya bayar da umarni rufe wurin biyo bayan samun rahotanni na sake farfadowar ayyukan hakar zinare ba bisa ka’ída ba a yankin.
ta cikin wata sanarwa da Jaridar Economic Confidencial ta samu, wadda tace jami’an hukumar sun gudanar da wani sumame ranar 16 ga watan Agusta a yankin unguwar District 2 Extension, in da suka sami nasarar kama mutum 16 da ake zargi.
Read Also:
Ta cikin sanarwar mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai ga minstan Segun Tomori ya ce wannan ya biyo bayan wata zinariya da aka samu a unguwar yayin da ake hakar masai a kusa da wani gida a yankin.
ya ce dakarun lura da hakar ma’adanai, karkashin Jagorancin John Atta Onoja, sun kafa shingen bincike na tsahon sa’o’i 24 a wuraren da abin ya shafa, har sai na kammala bincike a wuri.
takardar ta ambaci Alake na jan hankalin mazauna yankin game da hadarin gurbatar muhalli ga lafiyar jama’a da ke tattare da irin wadannan ayyuka, yana mai shawartarsu da su guji shiga wuraren da abin ya shafa har sai an kammala aikin tsaftace muhalli da tabbatar da doka.