Gwamnatin Tarayya Ta Jaddada Aniyarta na Kawo Karshen Matsalolin Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU)
Ministan ilimi Dakta Tuni Al’ada ne ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da manema labarai a birnin Abuja, inda ya ce shugaban ƙasa Bila Tinubu yana gudanar da wasu sauye-sauye, domin samun mafita ga kalubalen da ake fuskanta tsakanin kungiyar da Gwamnatin tarayya
Dakta Alausa ya ce, gwamnati ta shiga tattaunawa kai tsaye da ASUU, inda kwamitin da Yayale Ahmed ke jagoranta ya mika shawarwari, kuma an gudanar da taron manyan jami’an gwamnati domin nazari a kai.
Read Also:
Ministan ya bayyana cewa an kafa kwamitin kwararru bakwai karkashin Jagorancin Sakatare Janar na Ma’aikatar Ilimi, domin daidaita matsayar gwamnati kan shawarwarin da aka gabatar.
Ya jaddada cewa gwamnatin Tinubu ba za ta rattaba hannu kan yarjejeniyar da ba za ta iya aiwatarwa ba, ko ta daure Najeriya da igiyar zato.
Ministan ya kuma ce gwamnatin Tinubu za ta ci gaba da ganin cewa ba a sake samun taƙaddama da ASUU ba, tare da tabbatar da cewa daliban Najeriya suna ci gaba da karatu ba tare da barazanar Yajin Aiki ba.
Ba dai wannan ne karon farko da kungiyar ASUUta yi yunkurin tsunduma yakin aiki a Nijeriyar ba sakamakon abin da take kira rashin cika mata alƙawarin da Gwamnatin tarayya ta zaga cikawa.