Kotu a ƙasar Finland ta yanke wa ɗan Najeriya mai ‘rajin ɓallewar ƙasar Biyafara’, Simon Ekpa hukuncin ɗaurin shekaru shida a gidan yari bisa laifukan ta’addanci.
Kotun ta same shi da laifin ƙoƙarin harzuƙa jama’a da niyyar ta’addanci da kuma shiga cikin ayyukan ƙungiyar ta’addanci.
Kotun ta kuma same shi da laifukan zamba ta haraji da kuma karya doka wanda hakan ya sanya kotun ta yanke masa hukuncin ɗaurin shekara shida a gidan yari.
Kotun ta bayyana cewa Ekpa ya yi ƙoƙarin ƙarfafa rajin ɓallewar yankin Biyafara a kudancin Najeriya ta haramtacciyar hanya tsakanin watan Agustan 2021 zuwa Nuwamban 2024.
Kotun ta ce ya yi amfani da kafafen sada zumunta domin samun shigewa gaba-gaba a wannan fafutika.
Ƙungiyar ƴan-awaren ta kuma samar da wasu ƙungiyoyi masu ɗaukar makami, waɗanda kotun ta bayyana a matsayin na ta’addanci.
A cewar hukuncin, Ekpa ne ya samar wa waɗannan ƙungiyoyin makamai da abubuwa masu fashewa da harsasai ta hanyar wasu mutanensa.
Haka kuma, an same shi da laifin amfani da kafafen sada zumuntarsa wajen ingiza mabiyansa su aikata laifuka a Najeriya.
Kotun ta ce ya dikata duk wadannan laifuka ne ya yin da yake zama a garin Lahti na ƙasar ta Finland, sai dai ya musanta zarge-zargen.
Hukuncin da kotun ta yanke ba shi ba ne na ƙarshe, wanda ake zargin zai iya ɗauka ƙara zuwa kotu ta gaba.