Kofa ya sanar da ficewarsa da ga NNPP

Dan Majalisa Mai wakiltar kananan hukumomin Kiru/Bebeji a zauren majalisar wakilan Nijeriya Abdulmumin Jibril Kofa ya sanar ficewarsa daga Jam’iyyar NNPP.

ta cikin wata sanarwa da jaridar Politics Digest ta samu kofa ya dangwarar da shahadar Jam’iyyar ne bayan abinda ya kira sharin adalci da shugabancinta yayi masa.

Wannan dai na zuwa ne biyo bayan ikirarin jam’iyyar na korar sa daga cikinta bisa abinda ta kira karya dokokinta tare da gaza biyanta wasu kudade da ya kamata ya biya na hakkoki.

daga cikin abubuwan da Jam’iyyar ta yi wukar kugu da su na korar Kofa akwai wata hira da ya yi a ‘yan tsakaninnan da yake yabon shugaban kasa Tinubu wanda ba Dan Jam’iyyar sa bane, wanda ta ce hakan ya saba dokokinta.

Sai dai kuma Kofa ta cikin sanarwar ficewarsa daga Jam’iyyar yace matakin da Jam’iyyar ta dauka akan sa ya zo masa a matsayin ba zata, kasancewar yasan bai karya wata dokar Jam’iyya.

“ganawar da nayi da manema labarai cikin harshen hausa da turanci, ban fadi wasu kalamai da ya kamata jam’iyyar ta yi min wannan mummunan hukunci ba,” yace hasalima kalamansa sun bi sahun dokoki da tsarin jam’iyyar ya tanadar wanda yake kara dabbaka damar fadin ALbarkacin baka.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com