El-Rufa’i ya shigar da ƙorafi kan zargin ƴansanda da cin zarafi

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasiru El-Rufa’i, ya shigar da ƙorafi ga hukumar kula da ƴansanda kan zargin ƴansandan jihar da cin zarafi.

El-Rufai ya ce cin zarafin ya haɗa da aikata rashin ƙwarewa da amfani da muƙami ba bisa ka’ida ba, da kuma saɓa wa dokar Ƴansanda ta 2020 da ƙa’idojinta.

Wannan ƙorafi, wanda mai magana da yawu El-Rufa’i, Muyiwa Adekeye, ya fitar a shafinsa na X, ya nuna buƙatar gudanar da bincike mai zaman kansa kuma cikin gaskiya.

A cikin sanarwar, El-Rufa’i ya ce “ina shigar da wannan ƙorafin ne a matsayin ɗan ƙasa mai kishin ƙasa da kuma tsohon jami’in gwamnati da ya yi hidima a matakai na tarayya da na jiha.

Ya bayyana cewa wannan mataki yana da nufin tallafawa hukumar kula da ƴansanda wajen gudanar da ayyukanta na tabbatar da ɗabi’a mai kyau da ladabi a tsakanin jami’an ƴansanda.

El-Rufa’i ya kuma buƙaci hukumar ƴansanda da ta riƙa bincike da kuma hukunta duk wani jami’in da ya karya doka ko kuma ya yi amfani da mukaminsa ba bisa ƙa’ida ba.

“Wannan ƙorafi ya shafi babban sufeton ƴansanda na Jihar Kaduna da wasu jami’an da ake zargi da aikata wannan rashin ƙwarewa da cin zarafi.” in ji sanarwar.

“Ina kira ga hukumar da ta gudanar da bincike mai inganci kan waɗannan jami’a, wanda zai tabbatar da gaskiya da hukunta duk wanda aka samu da laifi.” in ji shi.

Ya bayyana cewa ya shigar da wannan ƙorafi ne don tabbatar da gaskiya, ladabi, da bin doka a ƴansandan Najeriya, tare da tabbatar da cewa dukkan jami’an ƴansanda suna aiki cikin ɗabi’a da biyayya ga doka da ka’idojin ƙasa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com