Hukumar DSS a Najeriya ta yi holen manyan kwamandojin ƙungiyar Ansaru da ta kama a watan da ya gabata, yayin da ake tuhumarsu da laifukan ta’addanci a babbar kotun tarayya da ke Abuja.
Waɗanda ake zargin sun haɗar da Mahmud Usman wanda aka fi sani da Abu Bara’a sai kuma Mahmud Al-Nigeri, wanda aka fi sani da Malam Mamuda.
Tuni hukumar ta shigar da ƙararraki guda 32 kan mutanen gaban mai shari’a Emeka Nwite.
Tuhumar da ake yiwa mutanen biyu akwai zargin haɗa kai da kuma tsarawa tare da ƙaddamar da hari kan gidan yarin kuje a watan Yulin 2022, wanda ya baiwa ɗaurarru sama da 600 damar tserewa.
Read Also:
Haka kuma sune ake zargi da kai hari kan barikin sojoji na Wawa da ke Kainji da ke jihar Naija, inda aka tafka asarar rayuka da dukiyoyi.
Hukumar ta DSS ta ce rahoton binciken ya nuna yadda waɗannan mayaƙa suka karɓi horo na musamman a sansanonin ƴan ta’adda da ke ƙasashen Mali da kuma Libya kan ƙaddamar da hari, sarrafa makamai da kuma dubarun yaƙi.
Mahmuda kuwa ya karɓi wani horo mai matuƙar haɗari a tsakanin shekarar 2013 zuwa 2015 a hannun wata ƙungiyar ta’addanci ta ƙasa da ƙasa.
DSS ta kuma ce waɗannan mutane biyu sune suka jagoranci manyan hare-haren ta’addanci da garkuwa da mutane ciki har da ɗaya daga cikin injiniyoyin ƙasar Faransa da ke aiki a Najeriya Francis Collomp a shekarar 2013 da kuma Alhaji Musa Umar Uba Magajin Daura a 2019.
Waɗannan mutane ne kuma suka kai hari kan guda daga cikin kamfanonin sarrafa Uranium a jamhuriyar Nijar.