Sojojin Nijeriya sun hallaka ‘yan ta’adda 6 a jihar Zamfara

Dakarun Operation FANSAN YAMMA sun sami nasarar hallaka ‘yan bindiga 6 a jihar Zamfara dake arewa maso yammacin Nijeriya, yayin da sojoji uku suka rasa rayukansu a harin kamar yadda PRNigeria ta gano

Wata majiya ta shaidawa mai sharhin kan harkokin tsaro Zagazola Makama cewa lamarin ya auku ne a karamar hukumar Bugudu yayin da dakarun Operation Base (FOB) da ke lilo suka fuskancin ruwan wuta a lokacin da su ke kokarin fitar da wata mota da ta makale a Fegin Rama.

An kara girke dakarun kawo dauki amma suka sake fuskantar harin kwantan bauna nan suka yi wata musayar wuta da ‘yan ta’addan

Majiyar ta tabbatar da cewa dakarun sojin sun ci karfin maharan, in da suka hallaka 6 daga cikin su, suka kuma tilastawa da dama guduwa domin cira da rayukansu, sai dai kuma sojoji 3 sun mutu a kokarin su na kare kasar daga hadarin ‘yan ta’adda.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com