Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta tabbatar da kashe jami’anta uku tare da bacewar wasu bakwai a wani mummunan harin kwantan bauna da aka kai wa rundunar kota-kwananta a jihar Benue.
A ranar Laraba 10 ga watan Satumban 2025 ne, aka kai wani hari makamancinsa a garin Egbe da ke ƙaramar hukumar Yagba ta yamma da ke jihar Kogi, a kusa da kan iyakar ta da jihar Kwara, inda jami’anta uku suka mutu.
Read Also:
Yayin da Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kogi, William Aya, ya tabbatar da mutuwar jami’an rundunar guda uku, sannan kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Miller Dantawaye, ya ce an tura tawagar da za ta mayar da martani zuwa yankin.
A wata sanarwa da rundunar ta fitar mai ɗauke da sa hannun jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, CSP Benjamin Hundeyin, a ranar Lahadi, ta ce ‘yan sandan sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar Juma’a, 19 ga watan Satumbar, 2025, a ƙaramar hukumar Katsina-Ala, inda inda ake kyautata zaton ‘yan bindigar yankin ne suka ƙaddamar da harin.
Kakakin ‘yan sandan ya ce an kama mutane shida da ake zargi a wani samame da ake ci gaba da kai wa kuma suna taimakawa da bayanai masu amfani.