Ƴan bindiga sun sako mutane 40 bayan sulhu da mahukuntan Katsina

Taswirar Katsina

Aƙalla mutane 40 da aka yi garkuwa da su ne suka shaƙi iskar ƴanci a ƙaramar hukumar Faskari ta jihar Katsina bayan tattaunawa tsakanin ƙasurgumin ɗan bindigar daji Isya Kwashen Garwa da mahukuntan jihar inda yaran ɗan ta’addar suka miƙa mutanen ga hukumomin jihar.

Bayanai sun ce sakin wannan adadi na zuwa ne bayan sakin wasu mutane 30 a Larabar makon jiya da kuma wasu mutum biyu na daban, wanda ke nuna a jumlace ɗan bindigar ya sako mutane 72 daga faro wannan tattaunawa kawo yanzu.

Mahukuntan Katsina na sahun waɗanda ke tattaunawa da ƴan bindiga don kawo ƙarshen tashe-tashen hankulan da jihar ke gani, sai dai a gefe guda ana ci gaba da ganin ta’adin waɗannan ɓatagari.

Mataimakin shugaban karamar hukumar Faskari, Hon. Isiyaku Wada ya tabbatar da sakin mutanen, to sai dai ya buƙaci haɗin-kan jami’an tsaro don tabbatar da samun nasarar wannan sulhu da ke bai wa kowane bangare damar yin walwala.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com