Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, ta halarci zaman zauren majalisar dattawan Najeriya, bayan dakatar da ita da aka yi na watanni shida.
A ranar Talata ne majalisar ta koma bakin aiki, bayan tsawaita lokacin komarsu da ƴan makonni.
Sai dai sanatar mai wakiltar kogi ta arewa ta halarci zaman majalisar ne wadda mataimakin shugabanta, sanata Barau Jibrin ke jagoranta.
tashar Channels TV ta ruwaito cewa, Shugaban Majalisar, kuma abokin rikicin Natasha, Godswill Akpabio bai halarci zaman majalisar ba. Ko da yake kafar bata bayyana dalilin rashin halartarsa ba.
Dakatar da ita ya janyo cece-kuce sosai a siyasar ƙasar, musamman saboda zargin cin zarafin da ta yi wa shugaban Majalisar Akpabio.