Gwamnan jihar Enugu, Peter Mbah ya fice daga jam’iyyarsa ta PDP tare da komawa APC mai mulkin Najeriya.
Mista Mbah ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai da ya shirya a fadar gwamnanatin jihar da ke birnin Enugu.
“Bayan dogon lokaci da muka ɗauka muna nazari, a yau mun yanke shawarar ficewa daga PDP tare da komawa APC,” kamar yadda gwamnan ya bayyana.
Mbah ya ce ya koma APC ne saboda kyawawan manufofin jam’iyyar da ayyukan ci gaba da take samarwa a Najeriya da ma jiharsa ta Enugu.
Gwamnan ya ce yana da ƙwarin gwiwar cewa komawarsa APC za ta samar wa jihar ƙarin damarmaki da ci gaba.
Taron ya samu halartar manyan ƴansiyasar jihar da suka haɗa da mataimakin gwamnan jihar, Barr Ifeanyi Ossai da tsoffin gwamnonin jihar, Sullivan Chime da Rt Hon. ifeanyi Ugwuanyi,da Tsohon Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Chief Ken Nnamani, da tsoffin ƴanmajalisar tarayya daga jihar da kuma masu ci, da shugaban majalisar dokokin jihar da shugaban jam’iyyar APC na jihar, da sauran muƙarraban gwamnatinsa, kamar yadda mataimaki na musamman ga gwamnan kan kafofin yaɗa labarai, Dan Nwomeh ya wallafa a shafinsa na X.
Dama dai tun jiya wasu daga cikin kwamishinonin gwamnan suka fice daga PDP tare da komawa APC.