Gwamnan jihar Bayelsa, Douye Diri ya fice daga jam’iyyarsa ta PDP; Diri ya bayyana haka ne ranar Laraba a gidan gwamnatin jihar da ke birnin Yenagoa lokacin taron majalisar zartarwarsa.
Cikin wata sanarwar ta sakataren yada labaran gwamnan, Daniel Alabrah ya wallafa a shafinsa na Facebook ya ce gwamnan ya fice daga PDP ne tare da ƴan majalisar dokokin jihar 19, ciki har da kakakin majalisar.
Kawo yanzu dai Gwamnan bai bayyana jam’iyyar da ya koma ba.
Ficewar gwamnan na zuwa ne kwana guda bayan da takwaransa na Enugu, Peter Mbah, ya fice daga PDPn tare da komawa APC.
A wannan shekarar kaɗai babban jam’iyyar hamayyyar ta PDP ta rasa gwamnoni uku, wani abu da masana ke kallo a matsayin babbar barazana ga jam’iyyar.