Babban ministan shari’a na Najeriya kuma babban lauyan gwamnati, Lateef Fagbemi, ya bayar da umarni ga hukumomi da dama su gudanar da bincike kan jerin sunayen masu laifin da shugaban ƙasar Bola Tinubu ya yi wa afuwa, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Fagbemi ya bayyana hakan ne a yayin taron Majalisar mahukunta da aka gudanar a ranar Alhamis, 9 ga Oktoba, 2025. in da ya ce hukumomin da za su gudanar da wannan binciken sun haɗa da hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (EFCC), hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi (NDLEA), da kuma Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya.
Ana hasashen cewa binciken zai iya kai ga cire fiye da rabin sunayen mutanen da aka yi wa afuwa.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu dai na jira a mika masa jerin sunayen da aka tantance domin ya sanya hannu na karshe, a yunkurin tabbatar da cewa duk wanda zai amfana daga afuwar ya cancanta.
Tinubu dai ya yi amfani da ikon da ƙundin tsarin mulki ya ba shi wajen yi wa mutum 175 da aka samu da laifuka daban-daban afuwa.











