Mai alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya bayyana cewa babu wasu bayanan da ke nuna cewa an yi wa masu bin wani addini ko Kirista ko Musulmi kisan ƙare dangi a Najeriya.
Sarkin ya faɗi hakan ne a yayin buɗe taron Majalisar Sarakunan Arewa a Birnin Kebbi, 2025.
Sarkin ya ce, “Babu yadda za a kashe wani mutum, ko Musulmi ko Kirista, ba tare da sanin sarakuna ko shugabannin al’ummar da wannan mutumin ya fito ba.”
Ya kuma ƙalubalanci kowa, a cikin gida ko waje, da su kawo hujja ta gaske kan wani kisan ƙare dangi a Najeriya.”
Sultan Sa’ad ya gargadi jama’a da kada su gaskata duk abin da suka gani ko karanta a kafafen sada zumunta, yana mai cewa yawancin bayanan da ake yaɗawa ba gaskiya bane.
“Yawancin abin da aka wallafa a kafafen sada zumunta ba gaskiya bane. Dole mutane su tabbatar da sahihancin bayani kafin su ɗauke shi a matsayin gaskiya,” in ji shi.
Sarkin ya bukaci Gwamnatin Tarayya da ta hanzarta tsara dokoki da za su kula da ayyukan masu amfani da kafafen sada zumunta domin rage yaɗa labaran ƙarya.










