Gwamna Jihar Katsina Dikko Radda ya amince da yin garambawul a kunshin majalisar zartarwar jihar tare da ƙirƙirar sabuwar ma’aikata da zata lura da harkokin kiwo a jihar.
Read Also:
Mai magana da yawun gwamnan, Malam Ibrahim Kaula-Mohammed, ne ya bayyana hakan ga manema labarai ranar Asabar a Katsina.
Ya ce Alhaji Adnan Nahabu an sauya masa Ma’aikata daga ta Harkokin Musamman zuwa Ma’aikatar Ilimin Gaba da Sakandare, Sana’o’i da Fasaha a matsayin Kwamishina.










