Ƙungiyar ma’aikatan lantarki ta Najeriya (NUEE) ta yi barazanar katse wuta a faɗin ƙasar, sakamakon zargin da take yi na cewa an kai wa ma’aikatan kamfanin rarraba lantarki na ƙasar hari.
Cikin wata sanarwa da muƙaddashin babban sakataren ƙungiyar, Dominic Igwebike ya fitar, ya ce hakan ya zama wajibi ne bayan zargin wasu ƴansanda da ke aiki bisa umurnin gwamnatin jiha, sun yi wa ma’aikatan da ke aiki a cibiyar lantarki ta Egbu da ke Jihar Imo duka, da yi musu barazana da bindiga da kuma garkuwa da wasu.
A cewar sa ƴan sandan sun shiga cibiyar ne da ƙarfin tsiya, tare da lalata kayayyakin aiki da dakatar da ayyukan da ake gudanarwa, kamar yadda kafar talibijin ta channels ta ruwaito.
A cewar sanarwar, ƙungiyar ta riga ta bai wa mambobinta umurnin katse samar da lantarki a jihar Imo har sai wani lokaci.
Ta kuma yi barazanar katse aiki a faɗin Najeriya har sai hukumomi sun ɗauki matakan gaggawa na tabbatar da tsaron ma’aikatan lantarki a faɗin ƙasar.











