Rundunar ƴansandan birnin Abuja, ta musanta wani iƙirari dake cewa wasu ‘yan bindiga sun yi yunkurin hallaka Laftanar Ahmed Yerima.
Wannan na cikin wata sanarwa da rundunar ƴansandan Najeriya, reshen birnin na Abuja ta fitar ta hannun kakakinta, SP Josephine Adeh, in da ta ce babu inda aka samu irin wannan iƙirari, labara ne kawai da bashi da tushe ballantana makama.
Da yammacin ranar Lahadi ne rahotonin yunƙurin kashe Laftanar Ahmed Yerima – matashin sojan da ya yi sa-in-sa da ministan Abuja, Nyesom Wike a makon da ya gabata – suka cika shafukan sada zumunta.
Read Also:
Rahotonnin sun yi iƙirarin cewa wasu matasa ne da ba a san ko su wane ne ba suka yi yunƙurin halaka sojan ruwan a Abuja, babban birnin ƙasar.
”Rundunar ƴansanda reshen Abuja ta lura da abubuwan da ke yawo a shafukan sada zumunta, da ke zargin an yi yunƙurin kashe Lt. Ahmed Yerima.
“Rundunar na son bayyana wa al’umma cewa ba mu samu wasu bayanai game da iƙirarin da ake yaɗawa ba ɗaukacin yankin Babban Birnin Tarayya,” in ji SP Josephine Adeh.
Daga bisani rundunar ‘yansandan ta shawarci al’umma su guji yaɗa labaran da ba su da tabbaci a kansu, saboda a cewarta babu abin da hakan ke haifarwa sai tayar da hankula.











