Bayanai daga jihar Neja na cewa maharan da suka sace ɗaliban makarantar St. Mary a kan babura suka je.
Sarkin Papiri, inda lamari ya faru ya shaida wa BBC cewa maharan sun je garin ne a kan babura inda suka karkasu.
”Wasu sun tsaya a bakin kasuwa, wasu kuma suka isa makarantar, inda suka harbe maigadin makarantar, wanda yanzu haka ke kwance a asibiti”,in ji shi.
Ya ce kawo yanzu ba a san adadin ɗaliban da aka sace be.
”Har yanzu ba a gama tantance adadin ɗaliban da aka sace ba, sai zuwa an jima ne in an kammala za a fitar da sunayen ɗaliban”, kamar yadda ya yi ƙarin haske.
Ya ƙara da cewa al’ummar garin na cikin tashin hankali da ɗimauta, tun bayan aukuwar harin.










